Gwamnatin tarayya ta zargi dan takarar shugaban kasa na
jam’iyyar Labour Peter Obi da cin amanar kasa, tare da
tunzura jama’a domin jefa Nijeriya cikin rikici bayan ya fadi
zabe.
Ministan Yada Labarai da Al’adu Lai Mohammed, ya ce babu yadda Peter Obi da Datti Baba Ahmed za su cigaba da yi wa ‘yan Nijeriya barazana da cewa idan aka rantsar da Bola Tinubu na jam’iyyar hakan ya na nufin kawo karshen dimokuradiya.
Lai Mohammed, ya ce wannan cin a amanar kasa ne, kuma ba za a bari su ci gaba da gayyato ta’addanci ba.
Wannan dai ya na zuwa ne bayan fallasar wani faifen murya, wanda a cikin sa aka jiyo muryar da aka ce ta Peter Obi ce ta na bayyana zaben shekara ta 2023 a matsayi yakin addini, lamarin da ya yamutsa hazon siyasar Nijeriya.