Jam’iyyar PDP ta zargi jam’iyyar APC da alhakin kitsa harin
da aka kai wa dan takarar ta na shugaban kasa Atiku
Abubakar a jihar Adamawa.
Idan dai ba a manta ba, a ranar Lahadin da ta gabata ne wasu da ake zaton ‘yan Boko Haram ne su ka kai farmaki a gidan Atiku Abubakar da ke birnin Yola ns jihar Adamawa.
Sai dai a wata sanarwa da PDP ta fitar, ta yi zargin cewa da ikirarin da wasu mahara su ka yi, an dauki nauyin harin ne don a raba Atiku da rayuwar sa a kan dagewar da ya yi na kwato zaben sa a kotun zaben shugaban kasa.
Wata sanarwa daga sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa Debo Ologunagba, ta nuna zargin cewa harin ya na iya samun nasaba da barazanar baya-bayanan nan da jam’iyyar APC ta yi.