Home Home PDP Ta Rubuta Wa Jami’an Tsaro Korafi A Kan Shirin APC Na...

PDP Ta Rubuta Wa Jami’an Tsaro Korafi A Kan Shirin APC Na Amfani Da Malamai A Kaduna

45
0
Jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, ta rubuta wa hukumomin tsaro takardar korafi, bisa zargin cewa jam’iyyar APC ta na shirin amfani da malaman addini domin yi mata gangamin zabe a masallatan Juma’a.

Jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, ta rubuta wa hukumomin tsaro takardar korafi, bisa zargin cewa jam’iyyar APC ta na shirin amfani da malaman addini domin yi mata gangamin zabe a masallatan Juma’a.

A cikin takardar korafin, jam’iyyar PDP ta yi gargadin cewa, hakan zai iya janyo barazanar zanga-zanga daga magoya bayan ta, lamarin da ta ce zai iya haifar da rikici a masallatai kamar yadda ta faru a jihar Katsina.

Jam’iyyar PDP, ta ce bai kamata wuraren ibada su kasance dandalin gangamin yakin neman zabe ba, ta na mai mamakin yadda jam’iyyar APC ta kwashe tsawon shekaru takwas a kan mulki, amma ba ta da dabarar neman kuri’a sai ta yi amfani da addini.

A cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na jam’iyyar Yakubu Lere ya raba wa manema labarai, PDP ta bukaci kungiyar Jama’atu Nasril-Islam ta shiraya wa manyan ‘yan takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna muhawara, domin tantance nagartar dan takarar da ya dace mutane su zaba.