Home Labaru Oyo-Ita Ta Nemi Alfarmar A Dakatar Da Binciken EFCC

Oyo-Ita Ta Nemi Alfarmar A Dakatar Da Binciken EFCC

266
0
Winifred Oyo-Ita., Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya
Winifred Oyo-Ita., Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya Winifred Oyo-Ita, ta roki alfarmar a dakatar da binciken da Hukumar EFCC ta fara gudanarwa bisa zargin zambar kwangila da aka yi ta naira biliyan uku.

Oyo-Ita, ta na rokon a ba ta damar yin murabus cikin mutunci,  duk ya ke ta amince da cewa ta gabatar da wasu manyan sakatarori da ke neman tallafi, ta na mai cewa ta aikata hakan ne ba tare da sanin cewa hakan zai iya haifar da matsaloli ba.

Ta ce ba ta mallaki wasu kamfanoni a boye ba, sannan ba ta da wasu manyan kadarori a birnin Abuja.

Dangane da bukatar ajiye aikin ta kuwa, Fadar shugaban kasa ta ce ba ta san da maganar ba, domin babu takardar neman yin hakan a halin yanzu kamar yadda mai Magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya bayyana.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/libertytvnews

Twitter: https://twitter.com/libertytvnews

Instagram: https://instagram.com/libertytvng

Liberty Radio 103.3 FM Abuja Kai Tsaye A Yanar Gizo ??

zeno.fm/libertyradioabuja

Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/tasharyancikaduna ?

Kira ??? +1-701-719-6971 don suraren (Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna) kai tsaye ta wayar hannu. Musamman Ga Waɗanda Suke Ƙasar Amurka.

Kuna iya turo mana labari ko shawara a: info@libertytvradio.com