Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Osinbajo Ya Kaddamar Da Shirin Tallafawa Kananan Masana’antu A Jihar Kebbi

Osinbajo Ya Kaddamar Da Shirin Tallafawa Kananan Masana’antu A Jihar Kebbi

Osinbajo Ya Kaddamar Da Shirin Tallafawa Kananan Masana’antu A Jihar Kebbi

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya kaddamar da wani shirin ba da tallafi ga kananan masana’antu a Jihar Kebbi.

Karanta Wannan: Shugabanci: Osinbajo Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa A Abuja

Osinbajo ya kaddamar shirin ne a kwalejin gwamnatin tarayya da ke Waziri Umar a Birnin Kebbi, wanda ofishin mataimakin shugaban kasa da na shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar Kebbi suka shirya.

Mataimakin shugaban kasa ya ce an samar da shi ne domin inganta kananan masana’antu zuwa kamfanoni, tare da  kara musu kwarin gwiwa da kuma kara samar da kudaden shiga ga gwamnatin tarayya da ta jihar Kebbi.

 Da ya ke  jawabi a wajen taron, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce manufar shirin shine, taimaka wa kananan ‘yan kasuwa domin samun sauki wajen rajista da hukumar yi wa masana’antu rajista da kuma amfani da bankin bada bashi ga masana’antu.

Kawo yanzu dai, jihar Kebbi dai ita ce jiha ta 24 cikin jerin jihohin da suka ci gajiyar shirin a karkashin ofishin mataimakin shuagaban kasa.

Exit mobile version