Ohaneze, ta umarci ’yan kabilar a fadin Najeriya su kaurace wa zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da ake shirin yi.
Wata sanarwa da Mazi Okechukwu Isiguzoro ya fitar a ranar Talata ta ce kungiyar Ohaneze Ndigbo ta gargadi masu zanga-zangar.
Ya bayyana cewa a tsawon tarihi, ’yan kabilar Igbo ’yan kabilar Igbo ne suka fi shan wahala bayan duk wata gagarumar zanga-zanga
a fadin Najeriya inda suke asarar rayuka da dukiyoyin su a fadin kasa.
Sanarwar ta ce, na farko dai, kalubalen tsaro da ake fama da shi a yankin Kudu maso Gabas zai hana gudanar da zanga-zanga a cikin aminci.
Isiguzoro ya kara da cewa zanga-zangar za ta kara ta’azzara matsalolin tsaro da ake fama da su a yankin Kudu maso Gabas,
Sannan za ta ba da dama ga masu aikata laifuka da makiyan al’ummar Igbo su yi amfani da zanga-zangar wajen haifar da rudani.