Home Labarai Ohanaeze Ta Gindaya Wa Zababben Shugaban Najeriya Sharruda

Ohanaeze Ta Gindaya Wa Zababben Shugaban Najeriya Sharruda

133
0

Kungiyar kabilar Igbo ta Ohanaeze, ta gabatar wa zababben
shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sharudda hudu idan har
ya na bukatar goyon bayan Inyamurai.

Babban sakataren kungiyar na kasa Okechukwu Isiguzoro, ya ce daga cikin sharuddan da su ka gindaya wa Tinubu akwai bukatar ya saki shugaban haramtacciyar kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu,

Isiguzoro, ya ce sakin Nnamdi Kanu daga gidan yari zai taimaka sosai wajen wanzar da zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabas.

Kungiyar, ta ce ya kamata Tinubu ya tabbatar da cewa an samar da shugaban majalisar dattawa daga yankin Kudu maso Gabas, kuma da zarar ya karbi ragamar mulki ya tabbatar da cewa an samar da jihohi akalla guda shida daga yankin Kudu maso gabashin Nijeriya.

Isiguzoro, ya ce akwai bukatar Tinubu ya tabbatar da cewa an samar da tsare-tsaren da za su habbaka tattalin arzikin yankunan kabilar Igbo, a kuma bude tashar jiragen ruwa ta Calabar sannan a tsaftace kogin Azumiri da ke jihar Abia, sannan a yi wa ‘yan kungiyar IPOB afuwa ya kuma biya diyya ga iyalan wadanda aka kashe.

Leave a Reply