Home Labarai Ofishin Kamfen Obi Ya Nuna Damuwa Kan Zargin Cin Amanar Kasa

Ofishin Kamfen Obi Ya Nuna Damuwa Kan Zargin Cin Amanar Kasa

63
0

Ofishin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na
jam’iyyar Labour, ya nuna damuwa a kan zargin cin amanar
kasa da gwamnatin tarayya ta yi wa Peter Obi.

Wannan dai, ya biyo bayan bayanan da ministan yada labarai Lai Mohammed ya yi a Amurka, cewa kalaman Peter Obi na cewa ba daidai ba ne a rantsar da Bola Tinubu ya zama cin amanar kasa.

Tuni dai Peter Obi ya yi watsi da zargin, tare da nuna takaicin cewa wasu na neman bata ma shi suna, ya na mai musanta faifan sautin da ya fito da zantawar sa da shugaban majami’ar WINNERS, Pastor Oyedepo.

Kakakin yakin neman zaben Peter Obi Yunusa Tanko, ya karfafa bayanan Obi, amma ya ce idan ma laifi ne kowane bangare ya aikata irin haka.

Yunusa Tanko, ya bukaci jami’an tsaro su tono wadanda su ka yi kwarmaton hirar salula ta Peter Obi domin ya na ganin su ke neman tada fitinar.

Leave a Reply