Home Labarai OBI YA CE SHARRI, BITA-DA-KULLI DA HASSADA CE AKE YI MASA DON...

OBI YA CE SHARRI, BITA-DA-KULLI DA HASSADA CE AKE YI MASA DON AN GA YA LASHE ZABEN 2023

3
0

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi, ya
soki kalaman da ake yadawa, cewa ya na tunzurz mutane da
ingiza su domin Nijeriya ta wargaje a nada gwamnatin rikon
kwarya don ya fadi zabe.

A cikin wata sanarwa da ofishin sa ya fitar, Peter Obi ya ce Kazafi da makirci da tuggu da hassada ce kawai ake yi ma shi, amma ba zai taba ingiza wasu su kawo wa Nijeriya cikas ba.

Duk da cewa an bankado wasu maganganun sa da ke nuna kiyayyar sa ga addinin musulunci, inda ya ke cewa zaben shekara ta 2023 Jihadi ne tsakanin Musulmai da Kiristocin Nijeriya, Peter Obi ya musanta cewa ya so ya ci da addini ne a takarar sa ta shugaban kasa.

Ya ce bai taba tattaunawa ko kwadaitar da wani ko wasu su yi wa Nijeriya zagon kasa ba, wadanda su ke yi su na yi ne kawai don su bata ma shi suna.