Home Labarai Obasanjo Ya Ce Ya Kamata Afirka Ta Sake Nazarin Dimokraɗiyyar

Obasanjo Ya Ce Ya Kamata Afirka Ta Sake Nazarin Dimokraɗiyyar

93
0
Obasanjo e1700490312862
Obasanjo e1700490312862

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obansanjo ya shawarci al’ummar Afirka su sake nazarin tsarin dimokraɗiyyar da Turawan yamma suka gadar musu.

ya bayyana hakan ne a wani taro kan dimokradiyyar nahiyar Afirka da aka gudanar a ɗakin taro na cibiyar ‘Yar’adua da ke nan Abuja.

Tsohon shugaban kasan, ya ce dole ne ƙasashen Afirka su gina tsarin dimokraɗiyyar da zai dace da al’adu da ɗabi’un al’ummar yankin.

Ya ci gaba da cewa lokaci ya yi da al’ummar Afirka za su ajiye tsarin da turawa suka gadar musu,

su gina nasu wanda zai dace da ala’dun su, ya ce yana da kyau shugabannin Afirka su nuna kishi kan ci gaban al’umomin su.

Obasanjo ya ce idan ana son dimokraɗiyya ya yi aiki a Najeriya da ma Afirka baki-ɗaya,

dole ne a gina shi kan tsarin shugabanci na gari, ta hanyar ba doka dama ta yi aiki.

Tsohon shugaban ƙasan dai ya ya dade yana sukar yadda ake gudanar da tsarin dimokraɗiyya a Najeriya da ma ƙasashen Afirka.

Leave a Reply