Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce ba tattaunawar siyasa suka yi da ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ba.
Olusegun Obasanjo, ya bayyana haka ne lokacin da yake gargadin magoya bayan Bola Tinubu kan yaɗa cewa ya marawa takarar Tinubu baya a ganawar sirri da suka yi a gidansa da ke Abeokuta ranar Laraba.
Tsohon shugaban kasan ya ce yaɗa irin wadannan labarai marasa tushe na lahani ga ‘yan siyasa irin su Tinubun.
A wata sanarwa da maitaimaka ma sa na musamman Kehinde Akinyemi ya fitar, ya ambato Obasanjo na cewa ganawar sa da Tinubu ta ‘yan uwantaka ce ba siyasa ba.
Tsohon shugaban kasa Obasanjo dai ya sake jadada cewa shi Uba ne ga duk ‘yan Najeriya da matasa da ke cikin matsi.
Wannan na zuwa ne dai bayan an ji shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a wajen wani taron jam’iyyar APC a Lagos ya na cewa ganawar Obasanjo da Tinubu alamar nasara ce gare su a zaben 2023.














































