Home Home NYSC Ta Magantu Kan Tura Masu Yi Wa Kasa Hidima Yaki A...

NYSC Ta Magantu Kan Tura Masu Yi Wa Kasa Hidima Yaki A Nijar

80
0

Hukumar kula da masu yi wa Kasa Hidima ta Nijeriya NYSC, ta ce babu wani shiri da ta ke yi na tura matasa masu hidimar kasa zuwa Jamhuriyar Nijar domin yakar sojojin da su ka yi juyin mulki.

Kakakin hukumar NYSC Mista Eddy Megwa, ya ce sun musanta batun ne sakamakon wani bidiyo da ake yadawa a shafukan sada zumunta, inda ya ce babu kamshin gaskiya a labarin da wani mai shirya barkwanci ya kirkira.

Ya ce ya kamata masu yi wa kasa hidima da iyaye su yi watsi da labarin da aka shirya da zimmar tada zaune tsaye.

Mista Eddy Megwa ya yi gargadin cewa, jami’an tsaro za su kama duk wanda ya kirkiri bidiyon.

Leave a Reply