Home Labaru Ilimi NYSC: Masu Bautar Kasa 26 Za Su Maimaita Aikin Yi Wa Kasa...

NYSC: Masu Bautar Kasa 26 Za Su Maimaita Aikin Yi Wa Kasa Hidima A Jihar Kano

615
0

Jami’in hukumar yi wa kasa hidima NYSC na jihar Kano Ladan Baba, ya ce dalibai 26 ne za su maimaita aikin yi wa kasa hidima a jihar Kano.

Baba ya bayyana haka ne, yayin da ya ke zantawa da manema labarai a wajen bikin yaye masu bautar kasa da su ka yi aiki a jihar Kano.

Ya ce a wannan shekarar, NYSC ta yaye dalibai dubu 1 da 942, wadan da su ka hada da maza dubu 1 da 220, da kuma mata 719.

Ladan Baba ya cigaba da cewa, daga cikin wadanda su ka yi aikin yi wa kasa hidima a Kano, dlibai 26 ne za su maimaita saboda kin zama a wuraren da aka tura su.