Rundunar tsaro ta Civil Deffence, ta bada kudi Naira miliyan biyu da dubu 800 ga iyalan marigayi Sufeto Iliyasu Abraham, wanda aka kashe lokacin da ‘yan bindiga su ka kai hari a gidan yarin Kuje.
Wannan dai ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar kuma Mataimakin Babban Kwamnada Olusola Odumosu ya fitar a Abuja.
Odumosu, ya ce Babban Kwamnandan Rundunar Ahmed Audi, ya bada cekin kudi na Naira miliyan biyu da rabi, da kuma kudi a hannu Naira dubu 300 ga matar marigayin da diyar sa.
Baya ga kudin, sanarwar ta ce Babban Kwamandan ya yi alkawarin daukar diyar marigayin Abimiku Abraham aiki a sabbin ma’aikatan da za su dauka nan gaba.
A karshe ya mika ta’aziyar sa ga iyalin, tare da tabbatar masu da cewa za a cigaba da tunawa da marigayin a matsayin jarumin da ya rasa ran sa ya na kokarin kare kasar sa.