Home Labaru NNPP Za Ta Kalubalanci Sanya Uba Sani A Jerin Sunayen ‘Yan Takarar...

NNPP Za Ta Kalubalanci Sanya Uba Sani A Jerin Sunayen ‘Yan Takarar Gwamnan APC A Kaduna

72
0

Biyo bayan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke da zama a jihar Kaduna ta yanke, na aminta da sunan Sanata Uba Sani a matsayin dan takarar gwamna na jamiyyar APC, da sauran ‘yan takarar 34 na mazabu, dan takarar gwamna na jamiyyar NNPP Sanata Suleiman Hunkuyi da jamiyyar sun ce za su kalubalanci hukuncin.

Sanata Hunkuyi da jam’iyyar NNPP ne su ka shigar da hukumar zabe kara, bisa sanya sunan Sanata Uba Sani a matsayin dan takarar jam’iyyar APC da sauran ‘yan takara 34 na mazabu.

A cikin takardar karar da NNPP da Hukunyi su ka shigar a kotun, sun ce APC ba ta gudanar da sahihin taron da ya fitar da wakilan da su ka yi zaben fidda gwani ba, wanda kuma har aka fitar da dan takarar gwamna da sauran ‘yan takarar mukaman majalisar dokoki na jihar Kaduna, inda su ka bukaci hukumar zabe kada ta sa sunayen su a matsayin ‘yan takara a zaben shekara ta 2023.

Yayin wani taron manema labarai a Kaduna, Hunkuyi ya ce NNPP ba wai ta kai karar APC ko ‘yan takarar ta ba ne, amma hukumar zabe ta shigar a gaban kotu bisa sanya sunan Uba Sani da sauran ‘yan takara 34.