Home Home NNPP Ta Maida Martani Game Da Dakatar Da Kwankwaso Daga Jam’iyyar

NNPP Ta Maida Martani Game Da Dakatar Da Kwankwaso Daga Jam’iyyar

22
0

Rikicin cikin gida na Jam’iyyar NNPP na ci-gaba da zafafa bayan da uwar Jam’iyyar ta bayyana korar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, mutumin da ya yi mata takarar shugabancin Najeriya a zaben da ya gabata.

Tun a makon jiya ne kwamitin amintattu na Jam’iyyar ya sanar da cewa, ya dakatar da Kwankwason tsawon watanni shida bisa zargin cin amanar Jam’iyyar a zaben daya gabata.

Kazalika, a litinin din nan, Jam’iyyar ta NNPP ta sanar da korar tsohon gwamnan na Kano saboda a cewarta, ya gaza bayyana a gaban kwamitin ladaftarwa domin kare kansa daga tuhumar badakalar wasu kudade kusan naira miliyan dubu guda.

Sai dai Hashimu Dugurawa dake zaman shugaban riko na reshen jihar Kano na Jam’iyyar ya ce tuni kwamitin koli na Jam’iyyar ya kori wadanda ke cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya yi ba dai-dai ba. Sai dai a jiya talata, jaridun Najeriya sun wallafa rahotan odar kotu dake hana korar Rabiu Musa Kwankwaso daga Jam’iyyar ta NNPP, kuma a cewar Farfesa Kamilu Sani Fage