Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

NLC Ta Yi Watsi Da Shirin Tinubu Na Biyan ‘Yan Najeriya N8,000

Kungiyar ƙwadago ta Nijeriya NLC, ta yi Allah-wadai da
matakin Shugaba Tinubu na neman amincewar majalisar
dokoki domin karbar rancen naira biliyan 500 daga Bankin
Duniya da nufin aiwatar da shirin da ta kira na bogi don rage
raɗaɗin ƙarin farashin man fetur da aka yi babu lissafi.

Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar NLC Kwamared Joe Ajaero ya fitar, inda ya ce shawarar biyan naira dubu 8 ga magidanta miliyan 12 a tsawon watanni shida cin mutunci ne da kuma wasa da haƙuri da imanin da su ke da shi a kan tattaunawa da gwamnati.

Ya ce rashin tunani ne gwamnatin da ta haddasa tsananin wahala a kan mutane cikin ƙasa da watanni biyu da hawan ta mulki, sannan ta zo ta kawo wani ƙudurin da ƙarara zai amfanar da masu kuɗin da ke riƙe da muƙaman gwamnati ba tare da duba halin da talakawa ke ciki ba.

Kwamared Joe Ajaero, ya ce abin da hakan ke nufi shi ne, gwamnati na neman hanyoyin da za ta sace dukiyar talakawa su kuma masu kuɗi su ƙara kuɗancewa.

Kungiyar NLC, ta ce ba za a lamunci waɗannan ƙudurori ga ma’aikatan Nijeriya ba, kuma matakin ya fi kama da kama- karya don haka ya saɓa da tsarin dimokraɗiyya.

Exit mobile version