Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Nisan Kwana: Yadda Muka Tsallake Rijiya Da Baya A Harin Jos – Matafiya

Kisan Gilla: NSCIA Da MURIC Sun Yi Allah-Wadai Da Hallaka Mutum 25 A Filato

Wani daga cikin matafiyan da aka tare aka kashe wasun su a Harin Jos, na Jihar Filato, a karshen mako, ya bayyana yadda maharan suka yi wa abokan tafiyar su kisan gilla bayan sun ritsa motocin su.

Mutumin ya shaida wa shirin Najeriya A Yau wanda Aminiya take gabatarwa ta intanet cewa da shi aka kwashe gawarwakin wasu daga cikin mutanen da aka kashe a motocin nasu zuwa asibiti kuma  Kafin su baro asibitin dai an samu gawar mutum 26.

Ya ce su da suka samu rauni sun kai mutum 29, sannan wadan su da yawa kuma da Allah Ya kiyaye ba a taba su ba.

Mutanen da aka yi wa kisan gillan a harin da aka kai musu  a kan hanyar Jos zuwa Zariya, suna hanyar su ta dawowa ne daga Bauchi, bayan sun kai wa Sheikh Dahiru Usman Bauchi ziyara domin murnar shiga Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1443 bayan Hijira.

A zantawar sa da shirin na Aminiya, kan harin na Jos, Shugaban kungiyar Fulani ta Gan-Allah Fulbe ta Kasa GAFDAN, Suleiman Yakubu, ya ce matafiyan sun fito ne daga sassa daban-daban na Kudancin Najeriya da ma kasar Ghana domin ziyartar shehin malamin.

Exit mobile version