Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Nijeriya Za Ta Goyi Bayan Shugaban Bankin Afrika Adesina A Karo Na 2

Nijeriya Za Ta Goyi Bayan Shugaban Bankin Afrika Adesina A Karo Na 2

Nijeriya Za Ta Goyi Bayan Shugaban Bankin Afrika Adesina A Karo Na 2

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Nijeriya za ta goyi bayan shugaban bankin cigaban Afrika Akinwumi Adesina a kokarin sa na sake neman shugaban banki a karo na biyu.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin yada labarai Femi Adesina.

Adesina ya ce, shugaba Buhari ya bayda tabbacin ne a lokcin da ya karbi bakuncin Akinwumi Adesina a fadar sa da ke Abuja.

Shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa, Nijeriya za ta hada kai da sauran shugabanni da masu ruwa da tsaki na bankin don ganin an sake zabar Akinwumi Adesina a karo na biyu.

Buhari ya ce zai yi haka ne sakamakon nasarori da Adesina ya samar a wa’adin mulkin sa na farko.

A baya-bayan nan dai, an hurowa Adesina wuta bisa zargin sa da nuna bangaranci a nade-naden wasu manyan mukamai a bankin, sai dai hukumar gudanarwar bankin ta wanke Adesina a kan zargin da ake masa.

Exit mobile version