‘Yan gudun hijirar Nijeriya da har yanzu su ke Kamaru, za su dawo gida da zarar kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin dawo da su tare da sake tsugunnar da su a arewa maso gabashin Nijeriya ya bada umarnin a cigaba da aikin kwaso su.
Shugaban kwamitin Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana haka, yayin da ya ke karbar rahoton da kwamitin ya gabatar a karkashin jagorancin Gwamnan jihar Borno Babagana Zulun a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A Cikin wata sanarwa da Kakain mataimakin shugaban kasa Laolu Akande ya fitar, ya ce an kwaso ‘yan gudun hijira dubu 4 daga kamaru zuwa Nijeriya kafin wasu dalilai su sa a dakatar da aikin.
Akwai dubban ‘yan Nijeriya da ke gudun hijira a kasashen da ke makwaftaka Nijeriya, wadanda su ka hada da Chadi da Nijar da kuma Kamaru, kuma ana fatan nan gaba kadan za a dawo da su gida.