Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Nijeriya Ta Dauke Wa Kamfanonin Da Ke Kera Motoci Masu Lantarki Biyan Haraji Na Shekara 10

Gwamnatin tarayya ta ce ta fito da sabon tsarin da zai yi wa
kamfanonin kera motoci da hada su a cikin gida rangwamen
biyan haraji.

Shugaban hukumar zayyana motoci da tsara su ta Nijeriya Jelani Aliyu ya tabbatar da haka, a wajen bikin baje-kolin motoci da kayayyakin su na kasashen Yammacin Afirka da aka gudanar a Legas, inda mataimakin sa Segun Omisore ya wakilce shi.

A wata sanarwa da y araba wa manema labarai, Jelani ya ce sabon tsarin ya na daga cikin gundarin tsare-tsaren da gwamnatin Nijeriya ta amince da su game da kera motoci a cikin gida.

Ya ce tsarin ya kunshi yafe wa kamfanonin da ke hada kayayyakin motoci biyan haraji na shekaru biyar, sannan gwamnati za ta yafe wa kamfanonin da ke kerawa da hada motoci masu lantarki biyan haraji na shekaru 10.

Jelani Aliyu ya kara da cewa, sabon tsarin na kamfanonin motoci zai yi aiki ne tsakanin shekara ta 2023 zuwa 2033, kuma babban burin tsarin shi ne samar da kyakkyawan yanayi ga kamfanonin motoci a Nijeriya domin samar da ci-gaba ta bangaren ayyukan da su ke yi.

Exit mobile version