Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta bude kofa ga duk mai sha’awar sayen manyan gidade da maka-makan filaye 160 a jahohin Nijeriya 12, wadada aka kwace daga hannun wadanda aka zarga da cin hanci da rashawa.
Tuni dai wasu sun fara kiran a gudanar da bincike wajen gano sahihancin kudaden wadanda za a sake saida wa irin wadannan kaddarori.
Mai magana da yawun hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya ce daga cikin kadadrorin akwai gidaje 24 da ke rukunin gidaje na Banana Island, da wasu 21 a Thornburn da Yaba da ke Legas, sai kuma wasu gidaje 6 da ke birnin Fatakwal.
A baya dai rahotanni dai sun ce, hukumar EFCC za ta yi gwanjon gidaje da filaye 144 da aka kwace a fadin Nijeriya, inda jihohin Legas da Abuja da kuma Jihar Ribas ke kan gaba.