Home Labarai Nijeriya: Ansaru Ta Haramta Harkokin Siyasa A Wasu Yankunan Kaduna

Nijeriya: Ansaru Ta Haramta Harkokin Siyasa A Wasu Yankunan Kaduna

117
0

Kungiyar ‘Yan ta’addan Ansaru, ta mamaye wasu Yankunan Gabashin karamar hukumar Birnin Gwari, tare da haramta gudanar da harkokin siyasa a Jihar Kaduna.

Shugaban kungiyar Ci-gaban Masarautar Birnin Gwari Ishaq Kasai ya bayyana wa manema labarai haka, inda ya ce yanzu haka kungiyar ta na daukar matasan yankin ta na kuma aurar da ‘yan mata.

Ya ce kungiyar ta na da sansanoni a mazabu 7 da ke Gabashin karamar hukumar, inda su ke lakada ma wadanda su ka gani da hotunan ‘yan takarar siyasa na kowace Jam’iyya duka a yankunan da su ke iko da su.

Ishaq Kasai, ya ce kungiyar Ansaru ta na samun karbuwa tsakanin mazauna yankin, lamarin da ke ba ta damar janyo hankalin matasa musamman a mazabun Tsohuwar Kuyello da Damari da ke mazabar Kazage, sannan ta gindaya sharruddan aure, wanda ya kunshi daukar amaren zuwa cikin daji ba tare da kayan gara ba, sai dai kawai katifa da kwanoni cin abinci kamar yadda ka’idar su take.

Ya zuwa yanzu babu wata majiyar hukuma da ta tattabar da ayyukan kungiyar a Birnin Gwari daga bangaren ‘yan sanda zuwa ma’aikatar tsaro ta jihar Kaduna.

Leave a Reply