Home Labarai Nijeriya Addu’a Ta Ke Nema Daga Amurka Ba Tsorata Mana Mutane Ba...

Nijeriya Addu’a Ta Ke Nema Daga Amurka Ba Tsorata Mana Mutane Ba – Magashi

39
0

Ministan Tsaro Bashir Magashi, ya ce Nijeriya ta na bukatar addu’o’i daga kasar Amurka ne ba su rika fidda sanarwar da za ta tada wa ‘yan Nijeriya hankali ba.

Magashi ya bayyana wa kwamitin tsaro na majalisar dattawa cewa, duk da cewa kwamitin tsaron kasa ya tattauna batun tare da shugaban Kasa ba a kyale shi haka kawai ba.

Ya ce idan aka ga hayaki to akwai alamar wuta a wani wuri, don haka ba za su yi shiru su dauki abin da wasa ba, za su maida hankali domin ganin wani abu irin abin da ake zargi ya auku a babbar birnin tarayya da sauran sassan Nijeriya ba.

Bashir Magashi ya shaida wa kwamitin cewa, tuni an umarci ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama ya gana da mahukuntan Amurka da sauran kasashe domin a rika samun fahimta a tsakanin kasashen.