Home Labaru Nijar: An Bude Taron Shugabannin Kungiyar Au A Yamai

Nijar: An Bude Taron Shugabannin Kungiyar Au A Yamai

690
0

Shugabannin kasashen Afirka sun kaddamar da yarjejeniyar cinikayya mara shinge a tsakanin kasashen a taron kolin Kungiyar Tarayyar Afirka dake gudana a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.   

Mutane kimanin dubu hudu ne da suka hada da shugabannin kasashe 32 da ministoci sama da dari ke halartar taron na birnin Yamai.

Wannan yarjejeniyar kasuwanci maras shinge na da burin bunkasa huldar cinikayya ta tsakanin kasashen Afirka 55 daga kaso 13 daga cikin dari da take a halin yanzu zuwa kaso 60 daga cikin dari nan da zuwa shekara ta 2022.

Najeriya da ke zama kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar, ta jima tana dari-darin shiga a cikin shirin, kuma za ta sa hannu a kan yarjejeniyar.

A yanzu dai daga cikin kasashen nahiyar 55, kasashen Benin da Eritriya ne kadai ke zama saniyar ware na kin shiga a cikin wannan wagegeyar kasuwa wacce ta kunshi mutane miliyan dubu da 200. Shugabannin kasashen na Afirka za su tattauna batutuwan da suka shafi ‘yan gudun hijira da kuma musamman batun matsalolin tsaro masu nasaba da ayyukan kungiyoyin masu da’awar jihadi da ke kara addabar wasu kasashen nahiyar.