Home Home Ni Na Kara Wa Kaina Maki A Jarrabawar Jamb – Mmesoma

Ni Na Kara Wa Kaina Maki A Jarrabawar Jamb – Mmesoma

72
0

Dalibar da ake zargin ta kara wa kan ta maki a jarrabawar share fagen shiga jami’a JAMB, ta amince da cewa da kan ta da sauya sakamakon jarrabawar.

Ejikeme Mmesoma, wadda tsohuwar ɗaliba ce a makarantar Sakandare ta ‘Anglican Girls’ a jihar Anambra, ta bayyana yadda ta kara wa kan ta maki a takardar sakamakon jarrabawar.

A ‘yan kwanakin nan dai lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce, tun bayan da hukumar da ke shirya jarrabawar ta karyata makin da dalibar ta yi ikirarin ta samu.

Hukumar JAMB dai ta ce dalibar ta samu maki 249, saɓanin maki 362 da ta ke ikirarin samu, amma ɗalibar ta kafe a kan cewa sakamakon da ta ke ikirari shi ne na gaskiya, lamarin da ya sa gwamnan jihar Anambra Charles Soludo ya kafa kwamiti domin gudanar da bincike.

Kwamitin ya gayyaci ɗalibar da shugabar makarantar da kuma jami’an hukumar JAMB domin jin bahasin kowane ɓangare, inda dalibar ta shaida wa kwamitin cewa ta amince da cewa da kan ta ta kara makin sakamakon jarrabawar ta, kuma ta yi amfani da wayar ta ne wajen sauya sakamakon jarrabawar.

STREAMING ADRESS

Ana sauraren Labarun ne kai tsaye, daga nan Tashar ‘Yanci a kan Mita 103.1

Za a iya sauraren mu a adireshin mu na yanar gizo

libertytvradio.com

Ko kuma a shafin mu na Youtube

youtube.com/libertytvnews

Ko a karanta Labarun mu a shafin mu na Facebook

Facebook) liberty tv

Ko a aiko sako kawai ta wannan lambar

08103679298

A dakace mu… TSOFAFFIN GWAMNONI 10 DA K

Leave a Reply