Home Home Neman ‘Yanci: Gwamnati Za Ta Nemi Tallafi Domin Ceto Fasinjan Jirgin Abuja...

Neman ‘Yanci: Gwamnati Za Ta Nemi Tallafi Domin Ceto Fasinjan Jirgin Abuja Zuwa Kaduna

59
0
Neman ‘Yanci: Gwamnati Za Ta Nemi Tallafi Domin Ceto Fasinjan Jirgin Abuja Zuwa Kaduna

An tashi baram baram a tattaunawar da ake tsakanin gwamnatin Tarayyar Najeriya da ‘yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasan da ke kan hanyarsa zuwa Kaduna daga Abuja, sakamakon dagewar da ‘ya bindigar suka yi cewa dole a yi musayar manyan kwamandojinsu da fasinjojin.

Rahotannin sun ce gungun ‘yan bindigar sun zake a kan musayar fasinjojin da suka yi awon gaba da su a ranar 28 ga watan Maris a katari ta jihar Kaduna a yayin da suke tafiya a jigin kasa.

Jaridar ‘Punch’ da ake wallafawa a najeriya ta ruwaito cewa an labarta mata aniyar gwamnatin kasar ta neman gudummawa daga kasashen waje don warware matsalar.

Kimanin mutane 8 ne suka mutu, wasu 26 suka samu rauni a yaayin da ‘yan  bindiga suka fasa layin dogo da bam a yayin da jirgin ke hanyarsa zuwa Kaduna.

ya zuwa yanzu ‘yan bindigar sun saki mutane 3 ne dga fasinjojin da suka sace, ciki har da shugaban banki manoma na kasar, AlwanHassan; sai kuma Sadique, da ga Farfesa  Abdullahi, shuguban kungiyaar dattawar arewacin Najeriya, sa kuma wata mata mai dauke da juna biyu da aka saki a  baya bayan nan.

Majiyoyin tsaro da ke da alaka da tattaunawar sun ce masalaha ta ruguje, sakamakon yadda ‘yan bindigar.