Home Labaru Neman Mukami: Majalisar Koli Ta Musulunci Ta Maida Wa Kungiyar Kiristoci Martani

Neman Mukami: Majalisar Koli Ta Musulunci Ta Maida Wa Kungiyar Kiristoci Martani

452
0

Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, ta yi wa Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya raddi biyo bayan kiran da ta yi wa Majalisar Dattawa da ta Tarayya ta na neman a ba Kiristoci manyan mukamai a shugabancin majalisa.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Larabar da ta gabata ne, kungiyar kiristoci ta Nijeriya ta yi ikirarin cewa, ba ta za taba yarda a ki ba Kiristoci ko da mukamin Shugaban Majalisar Dattawa ko na wakilai ko kuma Mataimakan su ba.

Da ya ke bayani a cikin wata sanarwa da ya fitar, Mataimakin Darakta Salisu Shehu, ya ce ya yi mamakin yadda kungiyar CAN ta rikide ta koma ta na jagaliyancin siyasa.

Ya ce kalaman da ta fitar rashin dattako ne da rashin sanin ya kamata, kuma zai iya kara rura wutar raba kan ‘yan Nijeriya.

Shehu, ya ce bai yi mamakin bayanin ba, domin Kakakin Yada Labarai na kungiyar CAN Adebayo Oladeji ne da kan sa ya rubuta a mamadin Shugaban kungiyar.

Ya ce ya kamata kungiyar CAN ta gaggauta zuwa ta yi rajista a matsayin ta na jam’iyyar siyasa, domin tuni ta kauce daga Kungiyar Kare Manufofin Addini ta koma jagaliyancin siyasa. 

Leave a Reply