‘Yan asalin Jihar Katsina mazauna Abuja, sun gudanar da zanga-zanga a birnin Abuja, inda su ka yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta dakatar da kisan-gillar da ake yi wa al’ummar jihar Zamfara tare da yawan garkuwa da su.
Katsinawan dai sun gudanar da zanga-zangar ne ranar Asabar da ta gabata, tare da nuna bacin rai, ganin yadda matsalar tsaro ke ta kara tabarbacewa ta hanyar yawaitar kashe-kashe da garkuwa da mutane da kuma kona gidaje da dukiyoyi.
Daya daga cikin wadanda su ka shirya zanga-zangar Fatimah Mustapha, ta ce sun fito ne domin yin kira ga gwamnati ta san cewa ana ci-gaba da yi wa jama’a kisan gilla da yawaitar garkuwa da mutane a jihar Zamfara.
Fatima, ta ce masu yin wannan ta’addanci, a kullum sai kara fitowa fili su ke yi su na aiwatar da kisa da garkuwa kai ba tare da ana daukar matakin gaugawa na kawo karshen fitinar ba.
Ta ce gwamnatin Jihar Zamfara ba za ta iya shawo kan fitinar ba, shi ya sa su ka yanke shawarar yi wa shugaba Buhari zanga-zanga a fadar shugaban kasa da ke Abuja.