Home Labaru Neman Inganta Rayuwa: Ficewar Da ‘Yan Najeriya Zuwa Kasashen Waje BaLaifi Ba...

Neman Inganta Rayuwa: Ficewar Da ‘Yan Najeriya Zuwa Kasashen Waje BaLaifi Ba Ne – Adesina

51
0

Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya ce bai ga wani abin tayar da jijiyoyin wuya ga ’yan Najeriyar da ke son barin kasar nan don neman ingantacciyar rayuwa ba.


Ya bayyana haka ne yayinzanatawa da Gidan talabijin na Channels wanda ya mayar da hankali kan nasarorin da gwamnati mai ci ta samu tun bayan darewarta karagar mulki a 2015.


Sai dai ya ce bai kamata a zargi gwamnatin Buhari kan yadda matasan kasar nan ke tururuwar barin Najeriya ba.


Adeshina yace “Idan mutum yana tunanin cewa yin hijira ita ce ta fi masa, to Allah Ya raka taki gona. Yace Amma bai kamata a ce tafiyar na nuna cewa akwai matsala a kasar nan ba”.


Ya kuma ce duk da yake mutane na barin Najeriya tun kafin zuwan gwamnati mai ci, akwai wadanda ko wanne yanayi aka shiga ba za su iya barin Najeriya.