Jami’an ‘yan sanda a jihar Enugu, sun yi amfani da barkonon tsohuwa a kan ma’aikatan wucin-gadi na hukumar zabe ta kasa, yayin da su ke zanga-zangar rashin biyan su hakkokin sun a aikin zabubbukan da su ka yi a jihar.
Wata majiya ta ce barkonon tsohuwar da ‘yan sandan su ka harba, ya shafi masu wuce wa da su ka hada da dalibai da masu ababen hawa, lamarin da ya sa su gudun neman tsira.
Masu zanga-zangar da su ka hada da matasa masu yi wa kasa hidima da dalibai da kuma ma’aikata, sun mamaye helkwatar hukumar zabe ta jihar tare da hana shiga ko fita daga ginin da ofishin ya ke.
Wata ‘yar bautar kasa Chioma Emmanuel, ta ce ba a biya ta ko sisi ba har yanzu, duk kuwa da ta yi aiki a zaben shugaban kasa da na gwamnoni, ta na mai cewa hatta kudin bada horo ba a biya ta ba.
Kwamishinan zabe na jihar Enugu Dakta Emeka Ononamadu, ya ce wasu ne su ka dauki nauyin matasan domin tilastsa hukumar zabe biyan su kudade bayan ba su yi aikin komai ba.