Home Labaru Neman Gafara: Tubabbun ’Yan Boko Haram Sun Roki ‘Yan Nijeriya Su Yafe...

Neman Gafara: Tubabbun ’Yan Boko Haram Sun Roki ‘Yan Nijeriya Su Yafe Masu

972
0

Wasu tubabbun ‘yan Kungiyar Boko Haram sun roki ‘yan Nijeriya su yafe musu ayyukan barnar da su ka tafka a baya.

Tubabbun ‘yan ta’addan sun bayyyana wa manema labarai haka ne, bayan sun kammala wani shirin sauya tunanin su, domin karkato su daga Boko Haram tare da koya masu sana’o’in dogaro da kai.

An dai ba su horon ne a Sansanin masu yi wa kasa hidima da ke Malam-Sidi da ke Karamar Hukumar Kwami ta Jihar Gombe.

Wani mai suna Bappah Nura da ya ce a baya shi manomi ne, amma daga baya ya shiga Boko Haram, ya ce ribbatar sa aka yi ya shiga Boko Haram, amma sai bayan ya shiga ya fahimci abin na su duk karya ce. Ya ce ya gode wa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari dangane da ba su damar samun horon sauya masu tunani tare da koya masu sana’o’in da za su dogara da kan su.

Leave a Reply