Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Neman Diyya: Al’ummar Gbagyi Su Ka Tare Wa Osinbajo Hanya A Abuja

Al’ummomin wani kauye da ke kusa da birnin Abuja, sun ce an kwace musu filayen noma da su ka gada tun iyaye da kakanni ba tare da an biya su diyya ba.

Mutanen sun bayyana haka ne, yayin da su ka mamaye hanya a daidai lokacin da tawagar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ke kan hanyar sa ta zuwa filin jirgin sama a Abuja.

Sun ce sun lura da cewa abin da aka yi masu ba kamar yadda ake yi wa sauran al’umma da su ka samu kan su a cikin irin wannan halin ne ba.

Daya daga cikin mutanen da aka kwace wa filin Hakimin Iddo Alhaji Sa’idu Sarki ya shaida wa manema labarai cewa, tun a shekarun baya gwamnati ta karbi filayen su ta ba sojoji amma ba a ba su diyya ba.

Basaraken, ya ce sakamakon karbe masu filin da gwamnati ta yi, yanzu ba su zuwa gona domin su yi noma, wanda hakan ya sa ba su samun abincin da za su ci.

Exit mobile version