Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki, ya zargi Adams Oshiomhole da amfani da wasu manya a fadar shugaban kasa wajen samun damar kafa shugabannin hukumar raya yankin Neja Delta NDDC.
Godwin Obaseki, ya ce Adams Oshiomhole ya sa an amince da shugabannin hukumar ne ba da sanin shugaban kasa ba.
Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin Kakakin sa Crusoe Osagie, ya na mai cewa Oshiomole ya aikata hakan ne a lokacin da shugaba Buhari ba ya Nijeriya.
Ya ce lokacin da shugaba Buhari ba ya Nijeriya, Oshiomhole ya samu manyan jami’an fadar shugaban kasa su ka amince ma shi da a kan shugabannin hukumar NDDC.
Mai magana da yawun gwamnan ya kara da cewa, yaran Oshiomhole ne su ka cika majalisar da aka kafa don ta rika lura da duk ayyukan hukumar NDDC.
Osagie,
ya ce hakan ya saba wa doka karara, domin abin da Oshiomole ya ke so shi ne, ya
cika burin sa na kakaba wanda zai iya juyawa a matsayin gwamnan jihar Edo, kuma
zai yi amfani da dukiyar hukumar NNDC ne don ya samu kudin da zai yaki
gwamnatin sa a lokacin zaben jihar.