Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

NECO Ta Saki Sakamakon Jarabawar Kammala Sakandare Ta 2022

Hukumar Shirya Jarabawar kammala sakandare ta Kasa NECO, ta saki sakamakon jarabawar kammala sakandare da aka yi a watan Yuli na shekara ta 2022 a fadin Nijeriya.

Shugaban hukumar Farfesa Danladi Wushishi bayyana haka a birnin Minna na jihar Neja.

Ya ce daga cikin dalibai miliyan 1 da dubu 209 da 703 da suka zauna jarabawar a bana, dalibai dubu 727 da 864 ne su ka samu akalla darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.

Ya ce idan aka kwatanta da sakamakon shekara ta 2021, inda dalibai dubu 878 da 925 su ka samu darussan turanci da Laissafi, a bana an samu raguwar sama da kashi 10 ke nan.

Exit mobile version