Home Home Nasara: Rundunar Sojan Sama Sun Kashe ‘Yan Fashi 34’ A Kaduna

Nasara: Rundunar Sojan Sama Sun Kashe ‘Yan Fashi 34’ A Kaduna

303
0

Rundunar sojan sama ta kasa ta ce ta kashe ‘yan bindiga fiye da 30 a kan Titin Sarkin Pawa da ke tsakanin jihohin Neja da Kaduna.


Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce sun yi nasarar kashe ‘yan bindigar da take kira ‘yan ta’adda ne sakamakon bayanan sirri da ta samu cewa wasu mahaya babura kusan 40 na tafiya a kusa da garin Akilibu zuwa Sarkin Pawa.


Sanarwar ta bbayyana cewa nan take jiragen sama suka far musu tare da karkashe su ta hanyar harba musu makaman roka.


Mazauna garin Mangoro da suka kai wa sojoji rahoto sun ce sun ga babura 17 da kuma gawar mutum 34 yashe a ƙasa.


Kazalika, mutanen sun ce sun ga bindigogi ƙirar gida 14 na ‘yan bindigar.

Leave a Reply