Fittacen attajiri kuma shugaban gidauniyar Dangote Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana damuwar sa a kan yadda talauci ya yi wa al’ummar Arewacin Nijeriya katutu.
Dangote, ya bukaci gwamnonin Arewacin Nijeriya su mike tsaye domin tunkarar lamarin a cikin gaugawa.
Attajirin ya bayyana haka ne, cikin jawabin da ya gabatar yayin taron tattalin arziki na jihar Kaduna karo na hudu da aka gudanar.
Dangote, ya kuma zayyana yadda fiye da kashi 60 cikin 100 na al’ummar Arewa ke rayuwa a cikin kangin talauci da kuncin rayuwa duk da irin arziki na kasar noma da su ka wadatu da ita. Aliko Dangote, ya yi kira ga gwamnonin Arewa su farga tare da tsayuwar daka wajen tunkarar matsin tattalin arziki da ya yi katutu a yankin su.