Bayan kwashe kusan wata huɗu suna zaman saurare, alƙalan kotun ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, sun shirya sanar da hukuncin da suka yanke.
Kotun wadda ke zamanta a Abuja, za ta sanar da hukunce-hukunce uku kan ƙararrakin da wasu ‘yan takara a zaɓen 25 ga watan Fabrairun 2023, suka shigar gabanta.
Atiku Abubakar, wanda yana daya daga cikin manyan wadanda suka shigar da kara daga babbar jam’iyya mai adawa ta PDP, da kuma na jam’iyyar LABOUR Peter Obi, wanda ya zo na uku, dukkan su suna ja da sakamakon da ya bai wa Bola Tinubu nasara a zaɓen.
Zaɓen wanda yana ɗaya daga cikin zabuka masu zafi da Najeriya ta gani, kuma da aka fi fafatawa tsakanin manyan ‘yan takarar, bai daina tayar da ƙura ba, da janyo muhawara musamman tsakanin magoya baya a shafukan sada zumunta.
Hukuncin kotun na zuwa ne daidai lokacin da shugaban kasa Bola Tinubu yake cika kwana 100 da hawa mulki.
You must log in to post a comment.