Home Labarai Najeriya Ta Buƙaci A Daina Ruwan Wuta A Gaza Nan Take

Najeriya Ta Buƙaci A Daina Ruwan Wuta A Gaza Nan Take

141
0
Yusuf Tuggar
Yusuf Tuggar

Najeriya ta yi Allah wadai da kisan fararen hula a Gaza, ta kuma yi kiran a gaggauta wanzar da zaman lafiya.

sanarwa da ministan harkokin wajen Najeriya, ya fitar ta ce gwamnatin ƙasa ta damu da halin da fararen hula suka shiga yanzu haka a Gaza,

Harin baya-bayan nan da Isra’ila ta kai kudancin Gaza a ranar Lahadi 26 ga watan Mayu ya kashe mutum aƙalla 45,

mafi yawan su mata da ƙananan yara, lamarin da ya ƙara yawan hare-haren da aka kai kan fararen hula tun bayan ɓarkewar yaƙin.

A sanarwar gwamnatin Najeriyar ta koka da yadda aka riƙa samun rashin mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da cin zarafin ɗan’adam,

Najeriya dai ta buƙaci a gaggauta komawa tsarin kiyaye ƴancin ɗan’adam, musamman hana kisan gilla da kuma kare fararen hula da ke Gaza .

Ta kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, da suka haɗa da Isra’ila da Hamas da kuma Majalisar Dinkin Duniya su ƙara mayar da hankali wajen kawo ƙarshen rikicin .

Leave a Reply