Home Labaru NAHCON Ta Kai Mahajjatan Nijeriya 7,844 Saudiyya Cikin Kwana 6

NAHCON Ta Kai Mahajjatan Nijeriya 7,844 Saudiyya Cikin Kwana 6

291
0
NAHCON, hukumar alhazai ta kasa

Kamfanonin jirage sama guda uku ne su ke gudanar da aikin jigilar mahajjatan, wanda suka hada da kamfanin MaxAir da Medview da kuma Flynas.

Kranta Wannan: Hajjin Bana: Hukumar Aikin Hajji Ta Kaduna Ta Sa Ranar Rufe Karbar Kudi

Mukaddashin sakataren hukumar alhazai ta kasa, kuma babban jami’i mai kula da walwalar alhazai a binrin Madina, Ahmad Maigari ya ce, jirage biyu ne suka taso daga jihohin Legas da Katsina, yayin da jirgi guda ya taso daga jihar Kano.

Maigari ya cigaba da cewa, an sauke mahajjatan ne a masaukin Markasiyya da ke Madina kusa da Masallacin Manzaon Allah S.A.W,  ya kara da cewa, i zuwa yanzu babu wani rahoto da aka samun akan rashin lafiyan wani alhaji ko hajiya.

A karshe Maigari ya yi kira ga mahajjata su yi hakuri wajen neman kamfanonin canji da suka yi rajista da su wajen samun canji kudaden su, inda ya gargade su su kiyayi neman canji a ko ina, don gudun fadawa hannun ‘yan damfara.

Leave a Reply