Home Labaru Kiwon Lafiya Nafdac Ta Bankado Magunguna Marasa Rajista Na Naira Miliyan 15 a Abuja

Nafdac Ta Bankado Magunguna Marasa Rajista Na Naira Miliyan 15 a Abuja

55
0

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa
NAFDAC, ta rufe shaguna biyu da ke dauke da magunguna
marasa rajista da ka iya rikita lafiyar kwakwalwa, wadanda
darajar su ta kai Naira miliyan 15 a farashin kasuwa.

A wani samame da ta gudanar a daya daga cikin wuraren da ke tashar mota ta Zuba a birnin tarayya Abuja, hukumar NAFDAC ta gano wani shago cike da magunguna marasa inganci da rajista.

Mataimakin darakta mai kula da bincike da tabbatar da doka na hukumar Mr. Tamanuwa Andrew Baba, ya ce galibin magungunan ko dai kwanakin ingancin su ya kare ko ba a yi masu rijista ba ko kuma su na da babbar illa.

Ya ce magungunan masu suna “Hajiya Aisha” ko “Hajia Salama” da aka gano, ana fasa kwaurin su ne daga kasar Ghana dauke da wani sinadari mai suna “Pyridine” da ke haddasa cutar daji da sauran cututtuka.