Home Labaru Nadin Sarautu: Wata Kotu Ta Sake Hana Ganduje Kafa Sabbin Masarautu A...

Nadin Sarautu: Wata Kotu Ta Sake Hana Ganduje Kafa Sabbin Masarautu A Kano

627
0

Wata babbar kotu a jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Ahmed Tijjani Badamasi ta hana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kafa sabbin masarautu a jihar.

Mai shari’a Badamasi ya kuma umurci gwamnan da ya janye daga nada kowa a matsayin sarki a sabbin masarautun da ya kirkira a kwanakin baya, sannan kuma ya bada umarnin a gaggawta aiwatar da odar ta hanyar wallafawa a jarida.

Idan dai ba a manta ba, wannan ita ce kotu ta biyu da ta bada irin wannan umurnin na hana gwamna Ganduje kafa masarautun Rano da Gaya da Bichi da Karaye.

Alkali Badamasi ya bada wannan umurni ne a ranar alhamins din da ta gabata, bayan wata kara da masu nada sarki a Kano su hudu suka gabatar, wanda suka hada da Sarkin Bai Alhaji Mukhtar Adnan da Makaman Kano Alhaji Sarki Ibrahim Makama da Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabahani da kuma Sarkin Dawaki Maituta Alhaji Bello Abubakar, dukkanin su dai suna kalubalantar kafa sabbin masarautu hudu a jihar da ganduje ya kirkira.