Home Labaru Nadin Ministoci: Shugabannin APC A Enugu Sun Ja Hankalin Shugaba Buhari

Nadin Ministoci: Shugabannin APC A Enugu Sun Ja Hankalin Shugaba Buhari

272
0
Shugaba Muhammadu-Buhari-2
Shugaba Muhammadu-Buhari-2

Jam’iyyar APC reshen jihar Enugu, ta shawarci Shugaba Muhammadu Buhariu ya nada jajirtattun ‘yan jam’iyyar kadai a matsayin ministocin da zai yi aiki da su a wa’adin mulkin shi na biyu.

APC ta ce ya zama dole shugaba Buhari ya janye daga duk wani kudiri na kawo ministocin da ba za su taimaka wajen ci-gaban jam’iyyar a jihohin su kamar yadda aka fuskanta a baya ba.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Enugu Dakta Ben Nwoye ya bayyana haka, a wajen taron shugabannin jam’iyyar da ya gudana a sakatariyar su da ke Enugu.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Enugu Dakta Ben Nwoye

Ya ce rassan jam’iyyar na jihohi a fadin Nijeriya sun fuskanci kalubale a wa’adin mulkin shugaba Buhari na farko, saboda zargin nada wadanda ba asalin ‘yan jam’iyyar ba ne a matsayin ministoci da sauran mukaman gwamnati.

Leave a Reply