Home Labaru Nadin Kwamishinoni: El-Rufai Ya Yaba Da Matakin ‘Yan Majalisa

Nadin Kwamishinoni: El-Rufai Ya Yaba Da Matakin ‘Yan Majalisa

710
0
Nasir El-Rufai, Gwamna Jihar Kaduna
Nasir El-Rufai, Gwamna Jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya nuna jin dadin sa da matakin ‘yan majalisar dokokin jihar da suka ki tantance wani a mukamin kwamishina.

A ranar Alhamis ne, shugaban majalisar jihar dokokin jihar Kaduna, Aminu Shagali, ya ki ba Aliyu Ja’afar kujerar kwamishinan noma, bayan an gano cewa ya kalubalanci gwamnatin shugaba Buhari a shekarar 2017.

Da yake magana lokacin rantsar da kwamishinonin na sa,        El-Rufai ya yaba wa ‘yan majalisar da irin hanyoyin da suka bi wajen tantance kwamishinoni.

Ya ce abinda ‘yan majalisar suka yi daidai ne, domin aikin su ne su rika duba duk abinda bai cancanta ba.

El-rufa’ai, ya ce mutum tara yake bai cika goma ba, dan haka yasa ake hadin guiwa da majalisar dokoki dan a samu cigaba.

Leave a Reply