Home Labaru Nadin Boss Mustapha: Matasa Sun Jinjina Wa Shugaba Buhari

Nadin Boss Mustapha: Matasa Sun Jinjina Wa Shugaba Buhari

298
0

Gamayyar kungiyoyin matasan Nijeriya, ta jinjina wa shugaba Muhammadu Buhari, sakamakon sake nada Boss Mustapha a matsayin sakataren gwamnatin tarayya a wa’adin mulkin shi na biyu.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, shugaban kungiyar Kwamred Nuhu Sani Lere, ya ce sake maida Boss Mustapha a kan mukamin shi, ya nuna karara cewa shugaba Buhari ya gamsu da kamun ludayin sa, musamman ta fuskar kokarin aiwatar da ayyukan ci-gaban Nijeriya.

Idan dai za a iya tunawa, a baya kungiyar ta sha babatun rokon shugaba Buhari ya cigaba da aiki tare da Boss Mustapha a wa’adin mulkin sa na biyu, duba da irin gudunmuwar da ya ke badawa ta fuskar ci-gaban kasa.

Nuhu Sani Lere, ya bayyana Boss Mustapha a matsayin irin mutumin da ‘yan Nijeriya ke bukata a daidai wannan lokaci, duba da yadda ya ke gudanar da ayyukan sa ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabilanci ba.Kwamred Nuhu Sani Lere, ya bukaci ‘yan Nijeriya su cigaba da ba gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari goyon baya, musamman a kokarin ta na shawo kan matsalar tabarbarewar tsaro da ta addabi kasar nan

Leave a Reply