Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nada Dr Thomas John a matsayin mukaddashin shugaban hukumar gudanarwa ta kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC).
Kamfanin NNPC ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya ce sabon nadin zai fara aiki nan take.
Sanarwar ta cigaba da cewa, Thomas zai rike mukamin ne har sai an nada sabon Minista ko karamin ministan man fetur domin fara aiki a matsayin shugaba, lamarin da ta ce hakan ya yi daidai da sashe na 1 (3) da sashe na 2 (1) na dokokin kamfanin NNPC.
Thomas John dai ya taba rike mukamin shugaban kamfanin NNPC, kuma jami’i a sashen gudanarwa na kamfanin.