Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci majalisar dattawa ta amince da nadin Farfesa Habu Galadima a matsayin sabon babban daraktan cibiyar koyar da dabaru da tsare-tsaren mulki ta kasa da ke Kuru a jihar Filato.
Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan ya karanto wasikar da shugaba Buhari ya aika wa majalisar yayin zaman ta na ranar Talata nan.
Buhari ya ce sashe na 8 (5) na dokokin hukumar ne ya ba shi ikon rubuta wasikar da ya aike wa majalisar a ranar 9 ga watan Yuli.
Shugaba Buhari, ya bukaci ‘yan majalisar su ba shi hadin kai wajen tabbatar da nadin Farfesa Galadima a matsayin shugaban Cibiyar ba tare da wata matsala ba.
Haka kuma, shugaba Buhari ya hada da takardun Farfesa Galadima da ke dauke da irin karatun da ya yi da gogewarsa a kan aiki da kuma duk wasu bayanai da za su taimaka wa majalisar wajen tantance shi.