Home Labaru Nada Kwamishina: JIBWIS Ta Yaba Wa Gwamnatin Jihar Filato

Nada Kwamishina: JIBWIS Ta Yaba Wa Gwamnatin Jihar Filato

645
0
Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, Shugaban majalisar Malamai Na Kungiyar Izatil Bid’ah Wa’Ikamatus Sunnah, JIBWIS
Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, Shugaban majalisar Malamai Na Kungiyar Izatil Bid’ah Wa’Ikamatus Sunnah, JIBWIS

Shugaban majalisar Malamai na kungiyar Izatil Bid’ah Wa’Ikamatus Sunnah wato JIBWIS, na kasa Shiekh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya ce mukamin kwamishina da gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong, ya ba daya daga cikin ya’yan kungiyar, Ustaz Muhammad Muhammad Abubakar, ya biyo bayan gudumuwar da kungiyar ke bayarwa ne wajen habaka mulkin dimukradiyya a Najeriya.

A zantawar sa da manema labarai a farfajiyar gidan  sa da ke daura da sakatariyar kungiyar a garin Jos Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yaba da hadinkan da ke tsakanin ya ‘yan kungiyar, wanda ya ce da wannan ne a ko wane lokacin zabe su kan sami nasarar zaben shugabanni na gari da ake kyautata zaton za su yi wa al’ummar kasa aiki.

Ya yi kira ga ‘ya’yan kungiyar JIBWIS su kara hada kai su mara wa gwamnati mai ci baya don ta sami kwarin gwiwar aiwatar da kyawawan manufofin ta na cigaban al’umma.

Sani Yahaya Jingir, ya ce gwamnan ya cancanci yabo bisa yadda ya sake ba al’ummar musulmin jihar dama dan su ba da tasu gudumuwar wajen tafiyar da ayyukan gwamnati ta yau da kulum dominn inganta rayuwar al’umma da bunkasa tattalin arzikin jihar.