Home Labaru Siyasa Na Ji Daɗin Yadda Manya Su Ka Gane Sauya Nijeriya Ba Aikin...

Na Ji Daɗin Yadda Manya Su Ka Gane Sauya Nijeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Ba Ne

126
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Nijeriya sun gane cewa sauya kasar nan aiki ne da ya shafi kowa.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya bayyana haka ne, a wajen wata liyafa da aka shriya domin girmama shugabannin kwamitin kasuwanci da siyasa da kafafen yada labarai da sauran ma’aikata.

Idan dai baa manta ba, a baya shugaba Buhari ya bukaci kusoshin Nijeriya su yi adalci wajen sukar lamirin gwamnatin sa, inda ya koka da cewa e ba su yaba wa mulkin shi duk kuwa a kokarin da ya ke yi.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, babu yadda za a yi mutum ya zauna ya na tunanin abin da ya wuce, don haka hakkin kowa ne a sama wa Nijeriya mafita matukar ana son alfahari da ita.