Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Na Amso Sakon Sirri Ne Daga Buhari Zuwa Ga Bagudu Da Sarkin Gwandu – Farfesa Gambari

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim
Gambari, ya ce ya je jihar Kebbi ne domin isar da wani sakon
sirri ga Gwamna Abubakar Atiku Bagudu da Sarkin Gwandu
Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar daga shugaba
Muhammadu Buhari.

Farfesa Ibrahim Gambari ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar Kebbi, inda su ka yi tattaunawar sirri da Gwamna Bagudu na kusan sa’a daya.

Ya ce shugaban kasa ne ya aike shi zuwa jihar Kebbi, domin su tattauna da Gwamna Abubakar Bagudu da Sarkin Gwandu.

Farfesa Ibrahim Gambari ya kara da cewa, shugaba Buhari na yin godiya da irin goyon baya da addu’ar da su ka yi ma shi a wa’adin mulkin sa.

Exit mobile version